Hot topics close

Premier League: Wasu wasan hamayya a kakar 2024/25 BBC ...

Premier League Wasu wasan hamayya a kakar 202425 BBC
Bayan da aka fitar da jadawalin Premier League da za a fara cikin watan Agustan 2024 - Ga jerin wasu wasannin hamayya da za a buga a kakar 2024/25.

Asalin hoton,

19 Yuni 2024, 08:52 GMT

Wanda aka sabunta Sa'o'i 2 da suka wuce

Ranar Talata aka fitar da jadawalin Premier League kakar 2024/25, wadda aka tsara za a fara daga 16 ga watan Agustan 2024 zuwa 18 ga watan Mayun 2025.

Manchester City ce mai rike da kofin bara, wadda ta kafa tarihin lashe hudu a jere a babbabr gasar tamaula ta Ingila.

Tuni aka samu ukun da za su buga gasar bana da suka hada da Leicester City da Ipswich Town da kuma Southampton.

Sun samu wannan gurbin ne bayan da Luton Town da Burnley da kuma Shieffield United suka yi ban kwana da wasannin da aka kammala.

Ga jerin wasu wasan Premier League na hamayya

Juma'a 16 ga watan Agusta - Man Utd da Fulham

Wannan shi ne wasan labulen bude kakar bana.

Wasan da suka buga a 2023/2024

  • Man Utd 1 - 2 Fulham
  • Fulham 0 - 1 Man Utd

Asabar 17 ga Agusta - Ipswich da Liverpool

Karon farko da Ipswich za ta buga Premier League bayan shekara 22 rabonta da gasar, kuma a lokacin da sabon kociyan Liverpool Arne Slot ke fara aiki.

Asabar 17 ga watan Agusta - Everton da Brighton

Za a kafa tarihi a Goodison Park a lokacin da matashin koci a karon farko zai ja ragamar wasan Premier League a Brighton & Hove Albion, Fabian Hurzeler mai shekar 31.

Lahadi 18 ga watan Agusta - Chelsea da Man City

Asalin hoton,

Wasan farko da Enzo Maresca zai ja ragamar Chelsea, wanda zai fuskanci tsohon mai gidansa, Pep Guardiola, wadanda suka yi aiki a Manchester City.

Litinin 19 ga watan Agusta - Leicester da Tottenham

Har yanzu Leicester City ba ta fayyace wanda zai ja ragamar kungiyar ba, balle a tantance wanda zai fuskanci Tottenham a King Power.

Asabar 24 ga watan Agusta - Aston Villa da Arsenal

Kociyan Aston Villa, Unai Emery ya doke Arsenal gida da waje a kakar 2023/24, sai dai wannan karon tun da wuri za su fara fuskantar juna.

Asabar 31 ga watan Agusta - Man Utd da Liverpool

Biyu daga manyan kungiyoyi Ingila za su kara a tsakaninsu, amma wannan karon Liverpoool mai sabon kociya da zai fara jan ragama, bayan maye gurbin Jurgen Klopp.

Asabar 14 ga watan Satumba - Tottenham da Arsenal

Wani wasa mai zafi da Arsenal za ta fuskanta da fara kakar da za mu shiga, wadda za ta buga fafatawar hamayya ta 'yan birnin Landan.

Asabar 21 ga watan Satumba - Man City da Arsenal

Asalin hoton, Reuters

City ce ta lashe kofin bara, Arsenal ta yi ta biyu - kungiyar Etihad ta lashe kofin na hudu a jere, Gunners kuwa ta yi shekara 21 rabonta da Premier League.

Asabar 21 ga watan Satumba - Southampton da Ipswich

Sabbin da suka hau Premier League a bana daga Champions League, kuma karon farko da za su fafata a gasar ta 2024/25.

Asabar 19 ga watan Oktoba- Liverpool da Chelsea

Sabbin kociyoyi ne za su barje gumi a karon farko a Premier League a tsakanin Slot daga Liverpool da kuma Maresca daga Chelsea, ko za su dora kan hamayyar da ke tsakanin kungiyoyin?

Asabar 23 ga watan Nuwamba - Leicester da Chelsea

Maresca ne ya kai Leicester Premier League a kakar da ta wuce daga Championship, daga nan Chelsea ta dauke shi, wanda zai fuskanci tsohuwar kungiyarsa a King Power.

Asabar 30 ga watan Nuwamba - Liverpool da Man City

Asalin hoton, Reuters

Daya daga wasan hamayya a Premier League, abin tambaya ko Slot zai kalubalanci Guardiola fiye da yadda Klopp ya yi a Liverpool?

Talata 3 ga watan Disamba - Arsenal da Man Utd

A irin wannan wasan a bara Arsenal ce ta yi nasara 3-1, karawar da ta kusan sa a kori Erik ten Hag, saboda kalubalen da ya biyo baya. Ko United za ta dauki fansa?

Asabar 7 ga watan Disamba - Everton da Liverpool

Wata karawar kalubale kuma karon farko da Slot zai buga wasan hamayya na Merseyside, ko yaya zai tarar da filin wasa na Goodison Park da yadda zai tsara doke Everton?

Asabar 7 ga watan Disamba - West Ham da Wolves

Karon farko da Julen Lopetegui zai fuskanci tsohuwar kungiyarsa Wolves, wadda ya bari a bara da cewar tana fama da matsin tattalin arziki, wadda ba za ta iya sayo manyan 'yan kwallo ba.

Wannan karon ya maye gurbin David Moyes a West Ham United.

Asabar 14 ga watan Disamba - Man City da Man Utd

Asalin hoton,

Wannan karawar za ta yi dan karen zafi, bayan da Manchester City ta mamaye Premier League, Manchester United ce ta dauki FA Cup da cin 2-1 a Wembley a bara.

Ko Ten Hag zai taka rawar gani a wasan, bayan da mahukuntan United suka amince ya ci gaba da horar da kungiyar Old Trafford kaka ta uku da zai shiga kenan.

Lahadi 29 ga watan Disamba - Ipswich da Chelsea

Za a buga wasa ne maimaicin haduwar da suka yi a Championship a bara, inda Kieran McKenna ke horar da Ipswich da kuma Maresca a Chelsea, wanda ya ja ragamar Leicester City zuwa Premier League.

Wasan da suka bara a bara Championship 2023/24

Litinin 22 ga watan Janairu 2024

  • Leicester 1 - 1 Ipswich

Talata 26 ga watan Disambar 2023

  • Ipswich 1 - 1 Leicester

Asabar 4 ga watan Janairu - Liverpool da Man Utd

Anan ma wata karawar ce ta hamayya, inda Slot zai karbi bakuncin Ten Hag a Anfield, watakila lokacin an ga kamun ludayin wanda ya maye gurbin Klopp.

Talata 14 ga watan Janairu - Arsenal da Tottenham

Asalin hoton,

Za a kara a Premier League bayan an kammala hutun buga wasannin FA Cup, shi ne wasa na biyu na hamayya na kungiyoyin Landan da za su fuskanci juna.

Asabar 1 ga watan Fabrairu - Arsenal da Man City

Arteta da Guardiola za su ajiye sanayya waje daya a kokarin lashe Premier League. Ana sa ran a kakar nan za su kara kalubalantar juna.

Asabar 22 a watan Fabrairu - Man City da Liverpool

Wata Fabrairu mai mahimmaci ne a Man City shi ne ke haska mata ko za ta lashe Premier League, amma wannan karon a cikin watan za ta kara da Liverpool.

Haka kuma a cikin watan za ta kece raini da Arsenal da Newcastle da kuma Tottenham.

Asabar 8 ga wata Maris - Man Utd da Arsenal

Arsenal za ta je Manchester United da sa ran za ta kara doke Ten Hag, bayan cin 1-0 a kakar da ta wuce a Old Trafford.

Laraba 2 ga watan Afirilu - Liverpool da Everton

Asalin hoton,

Slot a wannan karon zai karbi bakunci Everton a Anfield a wasan hamayya na Merseyside derby, lokacin ya kwan da sanin yadda ya buga wasan farko a Goodison Park.

Asabar 5 ga watan Afirilu - Man Utd da Man City

Wasan da Ten Hag zai karbi bakuncin Guardiola zai kayatar, domin fafatawa ce ta hamayya, wadda ake san Ten Hag zai taka rawar gani, bayan da aka yadda ya ci gaba da jan ragamar United.

Guardiola na fatan kara lashe Premier na biyar a jere, Ten Hag na so daukar na farko a United, wadda rabonta da kofin tun bayan Sir Alex Ferguson.

Asabar 10 ga watan Mayu - Liverpool da Arsenal

Wannan wasa ne na daf da za a kammala Premier League, watakila kowacce a lokacin na bukatar maki, kenan karawar sai an tashi.

Lahadi 18 ga watan May - Chelsea da Man Utd

Ko da yaushe Chelsea da Manchester City karawa ce ta hamayya, ko a bara an zazzaga kwallaye da yawa a raga - wasa na biyu za su buga ne a ranar rufe Premier League 2024/25.

Wasannin da suka buga a bara 023/2024

FA CUP Asabar 20 ga watan Afirilun 2024

  • Man City 1 - 0 Chelsea

Premier League Asabar 17 ga watan Fabrairun 2024

  • Man City 1 - 1 Chelsea

Premier League Lahadi 12 ga watan Nuwambar 2023

  • Chelsea 4 - 4 Man City
Similar news
News Archive
  • Karen Khachanov
    Karen Khachanov
    Karen Khachanov vs Stefanos Tsitsipas live score, updates ...
    27 Jan 2023
    2
  • Commercial aviation
    Commercial aviation
    Is the new Boeing 737 Max safe to fly? A new book makes you wonder.
    30 Dec 2021
    1
  • TSB
    TSB
    TSB give Taranaki shoppers a massive hand-out
    2 May 2022
    1
  • Peanut
    Peanut
    'A peanut slab in a jar' - Pic's and Whittaker's team up to create new spread
    21 Jan 2021
    2